April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Najeriya ta jaddada kudirin fitar da mutane miliyan dari a kangin talauci

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce za ta tallafawa kananan hukumomin kasar nan domin ragewa al’umma radadin talaucin da suke fama da shi a yanzu.

Ministan ayyuka na musamman Sanata George Akume ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar tsara yadda ake kashe kudaden gwamnati Victor Morakwu a ofishinsa a Abuja.

George Akume ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su samar da hanyoyin saukakawa rayuwar al’ummar dake zaune a karkara.

Ministan ya kara da cewa wannan shirin na daya daga cikin alkawuran da shugaba Buhari ya dauka na fitar da mutane miliyan dari daga kangin talauci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *