May 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Phima ta rufe wasu Asbitoci a karamar hukumar Gwarzo wanda ke gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba

1 min read

Hukumar Phima wacce ke kula da Cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano ta rufe Asbitocin da hukumar Bata gamsu da yadda suke gudanar da ayyukansu ba.
Aikin dai Wanda hadin Gwiwa ne da hukumar dake lura da magunguna dake ta sarrafi dasu ta Kasa.

Da yake jawabi Farfesa Salisu Ahmad ya ce sun kai ziyara wasu Asbitoci dake Garin Gwarzo Kuma mun tarar da su basu cigaba ka’idojin da aka shinfida ba, a sakamakon haka ne ya sanya muka rufe Asbitocin.

Ya Kara da cewa akwai Asbitoci da dama wadanda basu da kwararrun Ma’aikatan da zasu kula da lafiyar Al’umma, kawai suna gudanar da ayyukansu yadda suka ga dama batare da kula da illar da hakan kan haifar ba.

Farfesan ya ce akwai Asbitin da aka kafa shi batare da Sanin hukuma ba, a dan haka Shima mun rufe shi.

Ya Kuma bukaci alumma dasu ringa lura da irin Asbitocin da zasu ringa zuwa domin duba lafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *