May 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kedco ta rufe Transformadin Yan janbulo a daren Asabar-Bilal Nasidi Mu’azu

1 min read

Al’ummar Unguwar Kabuga da Buk Quarters, sun gudanar da wata zanga-zanga a daren jiya Asabar a sakamakon rufe transformar su da Kamfanin Kedco suka yi a daren jiya.

A cewar su suna zauna kawai sai suka ga ma’aikatan Kamfanin Kedco sun zo sun kashe wutar lantarkin ta su.

Mutanan dai sun ce kasu 95 na al’ummar Unguwar suna amfani da miter ne a Dan haka Basu ga dalilin da ya sanya kedco din dage transfemadin tasu ba.

Wasu Mutane da muka zanta da su sun Yi Mana Karin haske game da lamarin.
Alhaji nura Ali abayeto shine shugaban kwamitin Unguwar yayi Mana bayani kan lamarin.

Kan koken ne ya sanya muka tuntube kamfanin kedco din sai dai Mai magana da yahun hukumar Ibrahim Sani Shawai ya ce damu mutanan suje hukumar a gobe domin jin dalilin rufe musu transformadin tasu.

Ko a baya bayan dai sai da Kamfanin ya rufe wasu transformadin dake Unguwar Tudun Yola da kuma Dakata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *