April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Asbitin Best choice ya horos da masu sana’ar siyar da magani a Chemist hanyoyin kauda siyarwa al’umma gurbatattun magunguna

2 min read
Asbitin Best choice ya horos da masu sana'ar siyar da magani a Chemist hanyoyin kauda siyarwa al'umma gurbatattun magunguna

Kungiyar masu shagunan siyar da magani wato Chemist ta ce tana tana iya kokarinta wajan ganin ta fitar da batagari dake Cikin su.

Shugaban kungiyar masu siyar da magani shiyar Kano Municipal Kwamared Aminu Hikima ne ya bayyana haka a yayin taron fadakar da masu shagunan magani kan illar siyar da magani mara inganci da kwayoyi wanda Asibitin Best Choice ya shiyar a nan Kano.

Asbitin Wanda ke yunkurin kawo gyara a bangaren siyarwa da al’umma magani mai kyau domin bunkasa lafiya a matakin farko.

Kwamared Aminu Hikima ya kuma ce kungiyar tana bibiyar irin magungunan da masu shagunan ke siyarwa domin tabbatar da cewa an baiwa al’umma magani mai inganci.

Shugaban Aminu Hikima ya kuma yi karin bayani kan zargin da ake yiwa masu shagunan maganin na siyar da maganin da bashi mara lafiya yake so ba,inda a wani lokacin ake musanya musu da wani.

A jawabin sa shugaban Asbitin
Best choice Alhaji Auwal Muhammad Lawan ya ce makasudin taron shi ne kawar da harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yadda masu siyar da maganin zasu kauda kansu daga siyar da magani mara inganci ko mai sa maye.

A yayin bitar ta wuni daya dai an gabatar da da makalu da dama wacce ke nuni da cewa wajibine a kawo sauki a bangaren lafiya wanda shi ne kashin bayan gudanar da al’amuran rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *