April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Najeriya sun yi wa mayaƙan ISWAP da Boko Haram kwanton ɓauna

1 min read
Sojojin Najeriya sun yi wa mayaƙan ISWAP da Boko Haram kwanton ɓauna m

Rundunar sojin Najeriya ta kashe mayaƙan Boko Haram da na ISWAP yayin wani harin da ta kai musu a ranar Laraba.

Daraktan watsa labarai na sojojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne sanar da hakan a yau Alhamis.

Sojojin sun yi wa mayaƙan kwanton ɓauna ne a kan hanyar Kwadal zuwa Amuda bayan sun samu labarin hare-haren da mayaƙan ke kaiwa a yankunan, hakan ya sa sojojin suka jira su a wata maraba inda suka buɗe musu wuta.

Sojojin dai sun samu nasarar ƙwace bindiga samfarin machine gun da gurneti uku da kuma harsasai 62 da babur ɗaya da kekuna uku.

Ko a kwanakin baya sai da mayaƙan ISWAP ɗin suka kashe wani janar ɗin soji da wasu sojoji uku a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *