May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Al’unmar Musulmi zasu rike soyayyar Annabi Muhammad (S.A.W) da sun yi sallama da dukkan matsalolin da suke fuskanta – Malam Mai Ashafa

2 min read

Wani Malamin Andinin Musulunci a nan Kano, Malam Ibrahim Kabiru Mai Ashafa ya ce, matukar al’umma suka bi koyarwar Annabi Muhammad S.A.W to ko shakka Babu duk matsalolin da ake fuskanta zasu zo karshe batare da wani bata lokaci ba.

Malam Ibrahim Kabiru ya bayyana haka ne a yayin taron Maulidin Annabi Muhammad SAW wanda Alhaji Habibu Abubakar ya shirya a daren jiya wanda ya gudana a unguwar Tudun Yola C dake cikin karamar hukumar Gwale a nan Kano.

Malamin ya Kara da cewa dukkan matsalolin talauci da matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta zasu iya zuwa karshe matukar aka koma ga Allah.

Ya kuma ce dukkan wani lamari da al’umma ke sanan da cewa da dasu za su iya samu matukar ya siffantu da halayen Annabi Muhammad SAW da kuma irin ayyukan da sahabbansa suka fadakar.


Malam Ibrahim ya kuma ce, akwai abubuwa masu yawa wanda Annabi Muhammad ya koyar na kyauta da sadaka da tausayi wanda ya kamata su zama abin koyi ga al’ummar musulmi,wanda kuma ta hakane ne nasara zata tabbata ga al’ummar.

Shima da yake nasa jawabin Sheikh Muhammad Anwar Sheikh Sheikh Isyaku Rabi’u ya bayyana farin cikin sa, bisa shirya taron,inda ya ce shirya irin wannan taron abune mai muhimmanci tare da falala domin samun rabauta da Kara neman kusanci.

Da yake jawabi tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya ce,
tunasarwa na daya daga cikin ginshin lamari ga musulunci wanda ya kamata al’umma su ringa yiwa junansu a ko da yaushe.

Ya kuma godewa Malaman da suka gabatar da jawabai inda ya bikaci al’umma dasu ji tsaron Allah a dukkan ayyukansu na rayuwa.

Alhaji Habibu Abubakar shi ne wanda ya shirya taron maulidin tunawa da Watan da aka haifi Annabi Muhammad SAW, ya kuma bayyana cewa sun gaji shirya taron tun iyaye da kakanni wanda tsahon lokaci ana gudanar dashi.

Alhaji Habibu ya kuma bukaci al’umma dasu yi kokari suyi amfani da irin sakonin da malaman suka fadakar da al’umma wanda ta haka kawai zasu samu rabauta.


A yayin taron dai al’umma da dama ne suka halarta daga sassa da dama dake nan Kano,inda aka gabatar da makaloli da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *