May 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Buhari ya rushe shugabancin APC ya naɗa Mai Mala Buni shugaban kwamitin riƙo.

2 min read

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar ne ya dauki wannan mataki bayan da ya soke kwamitin rikon APC din a wani taro da ya gudanar a ranar Alhamis da rana.

Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ne, kamar yadda mai taimaka masa kan shufakan sada zumunta Bashir Ahmed ya fada a shafinsa na Twitter.

Jam’iyyar APC dai na ta fuskantar matsaloli a baya-bayan da suka shafi shugabancinta.

An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kuma Shugaba Buharin ne ya jagoranci taron.

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajoda gwamnaonin jihohi na jam’iyyar APC da mambobin Kwamitin gudanarwarta su ma sun halarci taron ta allon talabijin ta intanet.

Dama dai tun da farko wani ɓangare na jam’iyyar APCn ya ce taron da Shugaba Buhari ya jagoranta na ”ɓangaren Victor Giadom” a yau, haramtacce ne.

Sanarwar da shugaban APC na riko Mr Ntufam Hilliard Etagbo Eta da Sakataren riko Waziri Bulama suka sanya wa hannu ranar Laraba da almuru ta bayyana cewa “yaudarar” shugaban kasar aka yi ya amince cewa Mr Giadom ne sabon shugaban riko na jam’iyyar.

“Muna so mu bayyana ƙarara cewa mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa sun yi amannar cewa an bai a shugaban kasa gurguwar shawara ko kuma an yaudare shi ya amince da haramtaccen taron da wani mai suna Victor Giadom ya kira ranar 25 ga watan Yuni, 2020,” in ji sanarwar.

Ranar Laraba Shugaba Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *