May 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Har yanzu Nigeria bata kawo karshen Polio ba.

2 min read

A yayin da Hukumar Lafiya Ta Duinya ta ayyana cewa nan ba dadewa ba Afrika za ta zama nahiyar da babu cutar korona, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin jin labarin cewa babu mai sauran cutar shan inna a kasar.

Shugaban Hukumar Kula Da Lafiya a Matakin Farko a Najeriya Dr Faisal Shuaib – ya tabbatar wa BBC a ranar Alhamis 18 ga watan Yunin 2020 cewa, kasar ta karbi takardar shaidarta da ke nuna cewa babu cutar a kasar.

A wata sanarwa da Shugaba Buhari ya fitar ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka taimaka wa Najeriya a yakin ta da cutar, daga kan na cikin kasar har na kasashen waje, da ma wadanda suka taimaka da kudi da sarakunan gargajiya na arewacin kasar, inda can ne cutar ta fi kamari.

A shekarar 2016, kadan ya rage kasar ta zama wacce babu polio a cikinta, amma sai lamarin ya baci.

A cewar shugaban, ”an yi kusan shekara biyu ba a samu mai dauke da cutar ba,” sai dai sun ji an ce akwai masu cutar har yanzu a jihar Bornon da ke arewacin kasar.

Kusan shekara hudu bayan nan, Najeriya ta kai matsayin yin murnar kawar daga cutar polio a kasar, amma abu daya da mutane ke tambaya aransu shi ne me ya sa kasar ta shafe tsawon lokaci ba ta cimma hakan ba.

Me ya sa Najeriya ta dade ba ta kawar da polio ba?

Dr Shuaib ya yi wa BBC bayani kan matsalolin da suka sa Najeriya ta shafe shekaru da dama ba ta kawar da cutar ba da kuma abubuwan da suka yi don cimma hakan.

Yarda da camfi– A wasu lokutan wasu ‘yan Najeriyar na yin imanin cewa Turawa sun sanya wasu cututtuka a cikin riga-kafin cutar shan innan don sakawa a jikinsu. Sannan wasu sun yarda cewa riga-kafin cutar yana hana mata haihuwa.

Mafita kan hakan shi ne an shigar da shugabannin addini da sarakuna don su ilimintar da mutane kan alfanun riga-kafin. Sakamakon yarda da suka yi da wadannan mutane, sai mutane suka fara sauya dabi’unsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *