June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zan nemi ganin Shugaba Buhari kan matsalar tsaro – Gudaji Kazaure

2 min read

Wani fitaccen ɗan majalisar wakilai daga arewacin Najeriya, ya faɗa
wa BBC cewa zai nemi ganawa da shugaba Buhari don bayyana
masa halin taɓarɓarewar tsaro da wasu yankunan ƙasar ke ciki.
Honorabul Gudaji Kazaure ya ce yana da hujjoji da wasu ƙwararan
shawarwari da zai bai wa shugaban kuma ya yi imani za su yi amfani
wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da shi.
A zantawarsa ta shafin BBC Hausa Faceboo, kan matsayinsa game
da cutar korona wadda ta addabi duniya, Gudaji Kazaure ya koka kan
“yadda ake kurara cutar, (don kuwa) ba ta kai yadda ake kai ta ba”.
Wasu sun yi imani ɗan majalisar na amayar da ra’ayin ‘yan Najeriya
da dama ne, inda suke zargin cewa mahukuntan ƙasar na bai wa
annobar korona kulawar da ta fi sauran matsalolin ƙasar musamman
ma taɓarɓarewar tsaro.
Dan majalisar wakilan ya ce “Ka duba ka ga yadda aka bai wa
wannan cutar muhimmanci a kowacce jiha, a kowacce ƙaramar
hukuma ta Najeriya, aka fid da maƙudan kuɗi. Amma mutum nawa ta
kashe?”
Gwamnatin Najeriya ta rufe kusan duk harkokin tattalin arziƙin ƙasar
tsawon makwanni, bayan ɓullar annobar korona ranar 27 ga watan
Fabrairu.
Kuma har yanzu, ba a buɗe makarantu da zirga-zirga tsakanin jihohin
ƙasar da kuma harkokin sufurin jiragen sama ba, yayin da yawan
masu cutar ya ƙaru zuwa sama da 12,500.
An kuma ba da rahoton cutar ya zuwa yanzu ta kashe mutum 354 a
Najeriya.
Gudaji Kazaure ya ce ya yi imani kafin cutar korona ta kashe mutum
ɗaya a Najeriya, “‘yan bandit (‘yan fashin daji) sun kashe mutum
100”.
“Ka duba ka ga rannan a Sakkwato, mutum 70 fa rana ɗaya suka
kashe. A ina korona ta kashe waɗannan mutane cikin kwana ɗaya?
Ɗan majalisar ya tambaya.
A cewarsa irin kashe-kashen da ‘yan fashin daji suke yi su ne suka fi
damunsa a kan cutar korona wadda yake ganin an fi mayar da
hankali kanta a ƙasar.
Kalaman Gudaji Kazaure na zuwa ne kwana ɗaya bayan wata
sanarwar shugaban ƙasar wadda a ciki Buhari ke kira ga ‘yan fashin
daji su ajiye makamai ko kuma su kuka da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *