April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yadda wata mata ta kama barowo a Kano

2 min read

Wata mata mai suna Zulaihat Haruna da ke unguwar ja’oji a karamar hukumar Kumbotso ta kama wani barowa da yaje yi mata sata bayan doguwar kokawa.

Kano Focus ta ruwaito barawon mai suna Muhammad Isah ya shiga gidan nata a daren ranar Lahadi bayan da jama’a ke tafiya sallar dare.

Ta ce lokacin da barawon ya shiga tayi tsammanin babban danta ne Abba, kafin daga bisani ta fahimci cewa barawo ne.

Ta kara da cewa bayan da ta rike shi suna kokawa ne sai ya zaro karfe ya dinga caccaka.

“Duk da haka ban cika shi ba har sai da ‘yan Vigilante da al’ummar unguwa suka kawo min dauki aka kama shi.

“Kuma wannan ba shi ne karon farko da yake shigo mana gida ba, wancan azumin ma saida ya shigo amma ba a kamashi ba, sai a wannan lokacin,” a cewar ta.

‘Yan Vigilante sun kama dilan kwaya a kasuwar ‘yan Kaba

‘Yan bindiga sun kashe dan vigilante suka yi garkuwa da wata mata a garin Falgore

‘Yan daba sun kone gida jami’in Vigilante tare sassara kwamadansu a Kano

Shi ma da ake zargin Muhammad Isah ya ce yaga gidan a bude ne yasa ya shiga ya dauki waya.

Ya ce bayan da ya saci wayar ne sai matar gidan ta kamashi, da hakan yasa ya caka mata karfe don ya kubutar da kansa.

“Ni kadai na ke yi, kuma ina fata za a yi min afuwa ba zan sake aikata haka ba,” inji shi.

A nata bangaren rundunar vigilante ta ce ta kama wanda ake zargin ne bayan da ya da matar ta yi jarumta ta rike barawon bayan ya saci waya tare da ji mata raunuka.

Acewar sakataren rundunar da ke unguwar Ja’oji Isah Musa Murtala, da zarar sun kammala bincike za su aika da wanda ake zargin ga jami’an ‘yan sanda don girbar laifin da ya aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *