May 11, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

AHaramun ne biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane

3 min read

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan kuma mataimakin shugaban masallacin birnin tarayya Abuja Farfesa Ibrahim Makari ya ce haramun ne biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Bustandaily ta ruwaito Malamin ya bayyana hakanne ya yin tafsirin Alqur’ani da yake gabatarwa a babban masallacin Abuja ranar Asabar.

Maqari ya ce idan har Allah S.W.T zai hana baiwa makiya na yaki kudi don kar a karfafe su suci gaba da yakar musulmi, ina kuma ga mutanen da saboda zalunci da ta’addanci za su kama mutum suce sai an hada musu kudi za su sake shi.

“A don haka ku hada kudi ku bayar a saki wannan mutumin haramun ne, kuma laifi ne.

“Idan a cikin kudinsa ya ga dama ya cire ya fanshi kansa wannan shi ya ga dama, amma bashi ne abinda manzon Allah S.W.A ya zabar masa ba.

“Hadisin Abu Huraira na Muslim, wani mutum yazo ya samu manzon Allah S.A.W ya ce, mutum ne yazo yana son ya kwace kudina.

Manzon Allah S.A.W ya ce kada ka bashi, kada ka bari ya kwata, ya ce ya rasululla idan ya yakeni fa? Ya ce ka yake shi kaima.

“ Ya ce ya rasulullah idan na kashe shi fa? Ya ce yana wuta, ya ce idan ya kasha ni fa? ya ce kana Aljanna,” inji malam.

Ya kara da cewa a babin toshe kafar barna haramun ne kuma yana daga cikin mafi girman hanyar toshe wannan kafar mai yi yasan cewa duk abinda zai yi ba za a bada wannan kudin ba.

“A karshe shi zai yi wahala ya yi barnar kudin, sannan a abincin da ya baiwa mutumin da ya kama da lokacin sa da kuma harsashin da yayi amfani dashi wajen kisan, amma yasan cewa ba za a bada kudin ba.

“Wanda duk kuma aka kashe lokacinsa ne ya yi kuma shahidi ne dan aljanna,” a cewar sa.

Ya kara da cewa matukar al’umma ta tsaya akan wannan ka’idar da musulunci ya aje, za a magance bala’in masu garkuwa da mutanen.

Sai dai ya ce matukar mutane za su cigaba da bada kudi domin su fanshi ‘yan uwansu to masu garkuwa da mutanen za su cigaba da yi ne don samun kudin siyo wasu makaman tare da firgitar da mutane.

“Kuma za su cigaba da yin karfi ta yadda za su gagari al’umma da gwamnati, kuma mutuwa dole ce za ta zo idan ma baka tafi yanzu ba dole zaka tafi watarana,” a cewar Maqari.

Ya kuma ce idan har masu garkuwa da mutane suka kama mutum to da ma ce da Allah ya bashi domin ya gwada jihadi.

“Jihadi ne yazo mana a arha shahada ce Allah ya bamu kawai kayi addu’a Allah yasa mucika da Imani, Allah ya karbi shahadar mu shikenan.

“Amma bai kamata ka baiwa mutane kudi ba ka karfafe su,” a cewar sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *