April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gidajen Marayu 200 ne suka amfana da tallafin abinci – Indabawa kurmawa Development Association

1 min read

Kungiyar Indabawa kurmawa Development Association ta bukaci Al’umma musamman mawadata dasu dage wajen Tallafawa Marayu da zaurawa domin rage musu radadin rayuwa da suke fuskanta.


Shugaban Kungiyar Alhaji Aminu Sharif Dikko ne ya bayyana haka a yayin rabon tallafin abinci ga gidajen Marayu 200 a jiya.

A Yayin taron dai malaman Addinin Musulunci sun gabatar da Makalu kan muhimmancin Tallafawa Marayu da Kuma matsalolin da watsar da Marayu ke haifarwa inda Suka bayyana cewa Allah Ubangiji ne da kansu yayi bayani a cikin alqur’ani mai girma game da Marayu.

Sun Kuma ja hankalin Marayu da kada suyi amfani da cewa su Marayu ne su aikata wani aiki na barna.

Haka zalika sun bukace su dasu nemi ilimi da sana’a,
Ya Kara da cewa tallafin an same shi ne ta hannun wasu bayin Allah da suke baiwa Al’ummar gudunmawa.

Wasu daga cikin iyayen marayun da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su.

A Yayin rabon dai an Raba kayan abinci da suka Hadar da shinkafa Taliya da Kuma makaroni.

Al’umma da dama ne dai suka hallaci taron rabon tallafin abinci Wanda ya gudana a unguwar ta Indabawa kurmawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *