May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga uku a dajin Sambisa

1 min read

Rundunar sojin Najeriya da ke aikin yaƙi da ‘yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan bindiga uku tare da lalata sansanin ‘yan bindigar a dajin Sambisa.

Cikin wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran rundunar sojin ƙasa na Najeriya Onyema Nwachuku ya fitar, ya ce cikin waɗanda sojoin suka kashe har da ɗan ƙunar-baƙin-wake, tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 biyu.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a wani samamen na daban da sojojin suka kai sansanin ‘yan bindigar – da ke yankin Buluwa na ƙaramar hukumar Kukawa – sun kashe wani ɗan bingida guda tare da ƙwato bindiga guda ƙirar AK-47 da harsasai 14 da babur guda ɗaya da kayan abinci da sauran kayayyaki.

A baya-bayan dai matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan arewacin Najeriya, inda a karhsne makon da ya gabata wasu da ake kyautata zato mayaƙan Boko Haram ne suka sace wasu ‘yan gudun hijira fiye da 100 a jihar Borno.

Haka ma a ranar Alhamis ɗin da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar furamare da na ƙaramar sakandiren Kuriga a jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *