May 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu tasi sun fara yajin aiki a yau Litinin.

1 min read

Dubban jama’a ne aka bari cirko cirko a Afrika Ta Kudu, bayan da direbobin tasi suka tsunduma yajin aiki.

Direbobin kananan motocin kasuwar sun datse manyan hanyoyin da ke shiga biranen Johannesburg da Pretoria duk da girke yan sanda da aka yi.

Bukatarsu dai itace gwamnati ta tallafa musu, bayan da suka ce dokar kulle da ta biyo bayan bullar cutar Korona ta sa abin da suke samu ya yi kasa.

A baya gwamnati ta yi musu tayin tallafin dala 300 ga ko wanne dan tasi da ke da rajista, sai dai sun yi watsi da batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *