June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kwaso ‘yan Najeriya 167 daga Afrika Ta Kudu – Onyeama

1 min read

Yan Najeriya 167 na hanyar komawa gida daga Afrika Ta Kudu.

Ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama ne ya wallafa hakan a Shafinsa na Twitter inda ya ce tuni ‘yan Najeriyar suka baro filin jirgin O.R Tambo da ke Johannesburg zuwa Abuja.

Ko a kwanakin baya cikin wannan watan na Yuni sai da aka dawo da wasu ‘yan ƙasar daga ƙasashen Masar da Indiya.

Ya bayyana cewa fasinjoji 45 za su sauka Abuja cikin 167 da aka kwaso, sa’annan a wuce da sauran 122 zuwa Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *