July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu -yanzu aka gano maganin corona.

1 min read

v

Hukumar da ke sa ido a harkar lafiya a nahiyar Turai ta amince da wani magani mai suna Remdesivir, domin amfani da shi wurin magance cutar korona.

A shekarun baya dai an yi amfani da maganin wurin yaƙi da cutar Ebola, a halin yanzu kuma, ana nan ana ci gaba da gwajin maganin domin amfani da shi wurin yaƙi da cutar korona.

Hukumar da ke sa ido a harkar lafiya a nahiyar ta Turai ta amince a fara amfani da maganin a duka ƙasashen Turai.

Za a fara amfani da maganin ne kan ‘yan shekaru 12 zuwa sama masu fama da nimoniya da kuma waɗanda suke buƙatar a saka musu na’urar taimaka wa numfashi.

Sai dai kafin a fara amfani da maganin, sai Hukumar Tarayyar Turai ta bayar umarnin ƙarshe sa’annan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *