June 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasar Saudiyya ta hana zuwa filin

1 min read

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar Lahadi, za a saka dokar
hana shiga wasu wuraren ibada na ƙasar sai da izini.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa an ɗauki wannan matakin ne
sakamakon shirin da ƙasar ta ke yi na gudanar da Aikin Hajji da
mutane ƙalilan.
Jami’an tsaro a ƙasar za su hana shiga Mina da Muzdalifah da kuma
Arafat sai da izini.
An bayyana cewa duk wanda ya karya wannan doka, zai biya tara da
ta kai ta riyal 10,000, kimanin kuɗin Najeriya sama da naira miliyan
ɗaya kenan.
Jami’an kuma za su ci gaba da sintiri kan duka hanyoyin da ke kai
wa zuwa wuraren ibadar domin tabbatar da an bi dokar da kuma yin
tara ga waɗanda suka karya dokar.
A kwanakin baya ne dai ƙasar ta sanar da cewa kashi 70 cikin 100 na
waɗanda za su gudanar da Aikin Hajji na bana baƙi ne mazauna
Saudiyya sai kuma sauran kashi 30 ɗin ne asalin ‘yan ƙasar.
Ƙasar ta ce adadin waɗanda za su gudanar da Aikin Hajjin ba za su
wuce mutum 10,000 ba sakamakon daƙile yaɗuwar cutar korona.
Mutum 248, 416 ne suka kamu da cutar korona a Saudiyya, inda
kuma mutum 2,447 suka mutu tun bayan ɓullar cutar a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *