May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Sandan Kano sun kama masu kwacen 41 a jiya

1 min read

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kama wasu matasa 41 waɗanda ake zargi da ƙwacen waya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.
DSP
Kiyawa ya ce, ana zargin matasan ne da tare hanya a daren Asabar a daidai mahaɗar titin Ɗanagundi da ke ƙaramar hukumar Birni da Kewaye inda suka riƙa karɓe wayoyi a hannun mutane.
An samu matasan da babura guda huɗu da wuƙaƙe manya da ƙananan da kuma miyagun ƙwayoyi a cewarsa.

Wasu mutane ne dai suka bawa rundunar bayanai na sirri Wanda hakan ya baiwa rundunar nasarar kama matasan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *