May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu mata biyu sun rasa ransu a Kano bayan da gini ya fado musu a kasuwar kurmi a jiya

1 min read

Matan Wanda ‘yan asalin jihar Katsina ne,sun zo siyayyar kayan auren yar su ne jihar kano.

A jiya ne dai jihar Kano ta tashi da mamakon ruwan sama Wanda shi ne musabbabin faduwar ginin da ya kashe matan.

Jaridar Bustandaily ta zanta da wasu makotan wannan rumfa inda suka shaida mana cewa dama al’umma sun koka kan yadda aka gudanar da ginin rumfunan a kasuwar.

Shima sarkin kasuwar ya shaidamana cewa yanayin da ake ciki na ruwan sama a Kano na zama barazana ga rayuwar al’umma Wanda akwai bukatar Sanya ido kan yadda ake gudanar da gine-gine a wasu daga cikin kasuwanni a nan Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *