May 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Asuu na Shirin fara Gudanar da Yajin aiki fadin Nigeria

1 min read

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa ta ce za ta yi wa yajin aikin watanni tara da ta jingine kome sakamakon rashin cika alƙawarin da gwamnati ta yi musu.
Shugaban ƙungiyar ASUU reshen jami’ar Oyo, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai.
Ya ce, ko kaɗan uwar ƙungiyar ba zata aminta da wannan salo na wasa da hankali da gwamnatin tarayya take yi wa ƴaƴanta ba.
Farfesa Ayo ya ce, har yanzu akwai wasu daga cikin ƴan ƙungiyar ta su da ke bin Gwamnatin Najeriya bashin kuɗaɗen albashin su na kusan watanni 3 zuwa 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *