April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano: Mutane 167 ne suka kamu cutar fitsarin jini a mako guda- Bilal Nasidi Mu’azu

1 min read

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce, kawo yanzu mutane 167 ne suka kamu da cutar nan da ta ɓulla a wasu yankunan jihar.

A wata zanta wa da bustandaily Daraktan lura da cutuka na ma’aikatar Dr. Bashir Lawan, ya ce, tuni aka ƙara samar da asibitoci guda takwas domin lura da waɗanda suka kamu da cutar, wadda ya ce ana zargin tana da alaƙa da guba.

Asibitocin sun haɗa da, Asibitin zana, da asibitin koyarwa na Aminu Kano sai asibitin Ƙwararru na Murtala.

Sauran su ne asibitin Waziri Shehu Giɗaɗo, da kuma asibitin Sheikh Jidda da kuma babban asibitin garin Rano da wasu asibitoci biyu a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Dr. Bashir ya ƙara da cewa, yanzu haka cutar ta mamayi ƙananan hukumomi takwas da suka haɗa da ƙaramar hukumar Gwale da Birnin da Kewaye.

Sauran su ne ƙananan hukumomin Dala da Fagge da kuma Bunkure, da Dawakin Tofa da Gwarzo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *