May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marayu da zaurawa sama 150 sun amfana da tallafin Abinci -Usman Dalhatu

1 min read

Exif_JPEG_420

Kungiyar tallafawa marayu da zaurawa dake Unguwar Medile ta raba kayan abinci ga mutane sama da dari da hamsin a jiya a Asabar.

Shugaban Kungiyar Kwamared Usman Dalhatu ne ya bayyana Haka a yayin zantawar sa da manema labarai.

Alhaji Usman Dalhatu ya Kara da cewa suna samun tallafin ne daga hannun jama’a da Kuma manyan kungiyoyi dake sassa da dama.

Ya Kuma bayyana Kira ga sauran mawadata dasu himmatu wajen cigaba tallafawa marayu da sauran masu bukata ta musamman.

Wasu daga cikin mutanan da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su bisa tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *