May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gidajen Marayu da zaurawa 450 ne suka amfana da tallafin kayan abinci da kayan sawa – Usman Dalhatu

1 min read

Mai unguwa Medile C Alhaji Isah Yari, ya bukaci Gwamnati da sauran masu hannu da shuni hadi da Hakimai da masu unguwanni dasu dage wajen tallafawa Marayu da marasa galihu dake Unguwannin su.

Alhaji Isah Yari ya bayyana haka ne a yayin taron rabon tallafin abinci da na kayan sawa Wanda Kungiyar inwar tallafawa zaurawa da Marayu ta gudanar wanda ya gudana a ofishin Kungiyar dake Unguwar Medile.

Ya Kara da cewa akwai bukatar shigowar Al’umma dan ganin Marayu musamman a wannan yanayi da Al’umma ke cikin bukatar taimako ta ko wani bangare.

Da yake na sa jawabin Shugaban Kungiyar Alhaji Usman Dalhatu, ya ce, makasudun wannan tallafi shi ne inganta rayuwar mabukata domin su yi walwala kamar yara masu iyaye masu iyaye.

Ya Kuma yi kira ga sauran Al’ummar dasu shigo cikin wannan taimako domin samun rabauta a gobe kiyama.

Ya Kuma ce, gidajen Marayu el Sama da dari hudu da hamsin ne suka amfana da kayan abinci da kayan sawa.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su tare da godewa wadanda suka taimaka musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *