May 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Harsashin bindiga a Fadar Gwamnatin Kano ya jikanta Dan jarida a yayin da ake bikin Ranar Yancin Yan jarida ta duniya

1 min read

Dan jaridar dake aiki da gidan talabijin na jihar Kano ARTV mai suna Nazirun Idris Ya’u ya tabbatarwa da Premier
Radio faruwar lamarin, sai dai ya ce ba’a san daga inda aka harbo harsashin bindigar ba.

Ya kara da cewa harsashin ya masa rauni amma ba mai yawa ba, kuma tuni jami’an yan sanda a fadar gwamnatin Kano suka kaddamar da bincike kan lamarin.

Kawo yanzu fadar gwamnatin Kano ba ta ce komai ba kan wannan harbin bindiga da ya shafi dan jarida a fadar gwamnatin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *