May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan kasuwa a Nigeria na gudanar da zanga-zanga.

1 min read

‘Yan Najeriya da ke gudanar da kasuwanci a ƙasar Ghana sun yi zanga-
zangar lumana a gaban ofishin harkokin ƙasashen wajen ƙasar a
Abuja.
Masu zanga-zangar, waɗanda ke ɗauke da kwalaye ɗauke da rubutu iri
daban-daban na nuna fushinsu kan yadda hukumomin Ghana ke ci
gaba da rufe musu shaguna sun bayyana cewa lokaci yayi da
gwamnatin kasar ya kamata ta dauki mataki.
Masu zanga-zangar dai sun ce abin da ake yi musu a Ghana ya isa
haka, don haka ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki.
Ko a mnakon da ya gabata sai da aka rufe sama da shaguna 40 na baƙi
sakamakon gudanar da kasuwanci ba bisa ƙa’ida ba.
Dokar ƙasar dai ta haramta wa baƙi waɗanda ba ‘yan ƙasar ba buɗe
shaguna domin goggaya da ‘yan ƙasar wurin sayar da kayayyaki, amma
kuma ba a haramta wa baƙn dillancin kaya ba.
Ko a shekarar da ta gabata sai da wasu mutane daga ƙungiyar ‘yan
kasuwa ta Ghana suka kulle shagunan baƙi mazauna ƙasar, kuma
akasari shagunan mallakar ‘yan Najeriya ne da ‘yan China.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *