May 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani likita ya rasa ransa a unguwar Janbulo Link, bayan da wasu mata uku dake zargin masu kwacen waya ne sun farmasa

2 min read
Kano

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe Wani matashi Abubakar Tijjani Shu’aibu a Unguwar Janbulo Link.

Abubakar Tijjani Atiku wanda ya kammala karatunsa na physiotherapist a Birnin Kudu kuma,wanda tini aka bunne gawarsa a jiya Juma’a a mahaifarsa dake Jihar Jigawa.

Wasu labaran Saudiyya ta soke hukuncin kisan waɗanda suka kashe ɗan jaridar Jamal Khashoggi

Najeeeb Badayi M Sani Daya ne daga cikin wanda labarin ya akan idansu ya shai da mana cewa mutanan sun zo a babur ne su uku kuma ana zatan biyo Abubakar Suka yi domin su kwace wayar sa.

Wani labarin Wata a Jihar Kano Kotu ta zartar da hukuncin Kisa akan wani tsaho da ya yiwa yarinya fyade

Ya kuma ce a ‘yan kwanakin nan unguwar ta su tana fama da wannan matsala wanda ya ce zasu dauki mataki da gaggawa.

Shi ma wani matashi Amir wanda a kofar gidansu abin ya faru yayi wa jaridar bustandaily karin haske game da labarin.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne jami’in Hulda da jamaa na rundunar Yan sandan kano kuma ya tabbatar da faruwar labarin inda ya ce suna gudanar da abincike a akan labarin tare da binciko masu yan ta’addan.

Ko a cikin satin da mukai bankwana dashi sai wasu da ake zargin masu kwancen Waya ne suka afkawa wasu matasa da sara a unguwar,shima Wani dan Jarida dake aiki a freedom radio da wasu mutane uku sun rasa wayoyinsu a yayin da suka bar daya daga cikin su cikin jina jina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *